Na tsallake rijiya da baya - Ibrahim Mai Shunku

[email protected] 2020-11-12 05:49:20 Labarai

 

Fiattacen jarumin Kannywood Ibrahim Mai Shunku ya bayyana wata gagarumar jarabawar da ta same su da abokanan sa.

"Ranar Talata goma ga watan Nuwamba shekarar dubu biyu da Ashirin (10/09/2020) muka hadu da wata gagarumar jarabawar da banyi niyar bayyana ta a shafukan sada zumunta ba amma ya zama dole saboda muna bukatar addu'ar ku . 

Ranar ce muka hadu da abinda ya matukar saka mu a cikin damuwa a kan hanyar mu ta zuwa kaduna daga Abuja. Muka hadu da masu garkuwa da mutane inda suka bude mana wuta na kusan mintuna talatin ba sassautawa, wannan dalilin ya yi sanadiyyar rasa rayukun  sama da mutane goma, baya ga haka kuma su kayi  a won gaba da kusan mutane sama da goma shabiyar, a cikin tawagar tamu da kuma wasu mutane daban. 

Cikin mutanen da a kayi a won  gaba  da su  akwai hadimin shubagan kasar Najeriya  Alh. Abdullahi Abubakar Wali shugaban Kungiyar Nigerian youth organization (NYO) da sauran mutane da yawa. Muna bukatar addu'ar ku akan Allah ya kubutar da su " kamar yanda jarumin ya bayyana a shafinsa na Instagram 

Labarai masu kamanceceniya