Za mu fara farautar ‘yan fim a Youtube - Afakallah

[email protected] 2020-11-12 09:22:48 Labarai

 

Hukumar tace fina-finai ta jihar Kano ta ce za ta fantsama ayyukan ta zuwa cikin shafukan YouTube domin yin farautar masu saka fina-finai da suka karya dokar hukumar.
Isma’ila Na’abba Afakallah ya bayyana cewa hukumar ta gano masu shirya fina-finai na fakewa da wannan dama, domin kauce wa sharuddan hukumar.
Ya kuma ce hukumar ta gano wa su ma su shirya fina-finai su na kauce wa bin dokokin hukumar su na saka fim batare da an tace shi ba a hukumar. 
Haka zalika ya kara da cewar, hakan ya baiwa ma su shirya fim su na cin Karen su babu babbaka a shafin Youtube.

Labarai masu kamanceceniya