Sharhin Fim Din WAKILI

[email protected] 2019-09-03 09:43:55 Sharhin Finafinai

Yan wasa: Ali Nuhu, Falalu Dorayi, Aminu Momoh, Garzali Miko, Umar Gombe, Rabiu Daushe, Sulaiman Bosho, Tijjani Asase, Hadiza Gabon, Aisha Tsamiya, Hannatu Bashir da sauransu

Fim din Wakili labari ne na gaskiya wanda ake kokarin bayyana wata mummunar al’ada da tad ade tana ci wa al’umma tuwo a kwarya ata yin mulkin mallaka da wasu shugabanni ke yin a tursasawa mabiya. An shirya wannan labari cikin barkwanci da annashuwa, yadda zai ja hanakalin dukkkan wanda ya kale shi, ko ma da labari a aka ba ka. An yi amfani kawarewa wajen shirya wannan fim din domin kuwa kwararru masu shirya fim da masu aktin ne suka shirya shi.

Yadda aka rika cika silima wajen kallon fim din a duk inda aka nuna shi ya nuna yadda fim din ya samu kyakkyawan aiki da tsari. Fim din ya samu ciakkaiyar karbuwa ga dukkan bangarorin al’umma, sarakuna da masu kudi da ma talakawa.

A cikin shirin, Sulaiman Bosho (Wakili) shi ne ya fito a matsayin basarake, wato Dagaci, wanda ake kiransa Wakili a cikin shirin, sannan babban Wazirinsa shi ne Falalu Dorayi wanda yake take masa baya da shirya masa yadda zai yi duk abin da yake so.

Daga cikin ayyukan da Wazirinsa (Falalu Dorayi) yake taimaka masa wajen aikatawa, akwai nemo yadda za a shawo kan mace idan ya ganta yana so. Akwai inda Wakili ya ga Hannatu Bashir yana so, kuma yana so yayi mata Ingilishi amma bai iya ba, sai Wazirinsa (Falalu) ya rubuta maganar da zai yi a allo ya tsaya a bayan Hannatu ya daga allon, shi kuma Wakili yana karantawa.

Da abu ya kai abu, sai Wazirin ya dauki Wakili ya kai shi wajen wanda yake koyar da soyayya na zamani (Umar Gombe) domin ya koya masa yadda zai rika shawo kan mata ’yan zamani cikin sauki. Nan take malamin soyayyar ya fada wa Wakili cewa babin farko wajen sace zuciyar mace shi ne sakin fuska, Wakili ya ce, “Basarake ba ya son raini.” Sannan aka ce dole ya saki fuska sannan ya kashe mata ido, inda shi ma waziri ya ce, “Ai kashe ido iskanci ne.”

A dayan bangaren kuma, akwai Garzali Miko (Tela) wanda Wakili ya yi amfani da shi wajen auren kisan-wuta, domin Hadiza Gabon (’Yar Hidimar Kasa NYSC) ta shaida wa Wakili cewa aurenta ya mutu kuma tana son komawa gidan mijinta. Garzali ya amince ya aure ta, amma kuma ba ta bin dokokinsa, inda har yake ce mata yawan fita da take yi tana yi a wuta, nan take ta ce masa, “Ai kai ne babban dan wuta, ba ka san auren kisan-wuta ka yi ba?”

A wani bangaren, Ali Nuhu shi ne ya fito a matsayin Alkali mai son neman zabi. Da Wakili ya je wajensa da zabi, sai Alkali ya tambaye shi, sai ya ce, “Ai na san ba ka karbar cin hanci. Da kai da cin hanci kamar Gabas da Yamma ne.”

Sai Ali Nuhu ya ce ya ce masa ai ya fi son ya daure na kusa da shi domin ya nuna darasi a kan sauran. Da sauran fuskoki da suka fito da jigon fim din. Fim din ya tsaru matuka, domin an yi amfani da gwanintar harshe wajen isar da sako cikin sauki da nishadi domin ba kowa ba ne yake iya isar da sako cikin barkwanci kuma sakon ya isa, musamman inda aka yi amfani da kirkira.

A karshen Wakili ya fara zuwa, inda ya shiga tarkon Tijjani Asase, nan take Wakili da Wazirinsa suka fara waka suna cewa, “Ye! Mai Girma Yesu na tuna da laifina!” Haka kuma a inda Wakili yake son ya nuna cewa yana da masaniya a kan asalin NYSC, sai ya ce, “Asalin NYSC wani Bature ne mai suna Albaro Morata ya kirkiro shi.”

Daga cikin abubuwa da za a koya a cikin fim din akwai: Labarin ya nuna cewa sarakuna suna da matukar tasiri a cikin al’umma, musamman Hausawa, don haka ya kamata su rika yin adalci da nuna natsuwa. Kamar yadda Hadiza Gabon ta kawo kukan cewa aurenta ya mutu kuma tana so ta koma gidan mijinta, inda Wakili ya nuna cewa idan auren kisan-wuta take so, shi ma zai iya kashe mata wutar tunda yana da mulki.

Fim din kuma ya nuna cewa komai nisan jifa kasa zai dawo da sauran darussa da za a koya masu dimbin yawa a cikin shirin. Duk wanda ya kalli fim din, zai tabatar da cewa fim din ya nishadantar da masu kallo, wadanda ba su kalla ba, kuma sai hanzarta su nemi fim din domin su nishadantu.

Daraktan fim din shi ma ya yi kokari wajen jagorantar fim din, sannan wadanda suka dauki nauyin fim din sun yi kokari wajen amfani da manyan kyamarori don daukar shirin. Sannan an yi amfani da wakokin gada irin na al’adar Bahaushe masu fadakarwa.

Wani abin burgewa da fim din shi ne yadda aka yi amfani da kyamarori manya na zamani musamman lura da yadda sauti ya fito radau, hoto ya fito garau, sannan kowane dan wasa ya yi kokari wajen nuna kwazo. Sannan uwa uba, Daraktan fim din Falalu A. Dorayi wanda yake shirya fina-finan barkwanci da suke yin fice irin su, Namamajo da Andamali da sauransu ya yi matukar nuna bajinta wajen isar da sako mai girma cikin nishadi da barkwanci.

Labarai masu kamanceceniya