Naziru Sarkin Waka ya sake gurfana a gaban kotu

[email protected] 2020-11-04 12:58:18 Labarai


Hukumar tace fina-finan Hausa ta jihar Kano ta sake gurfanar da Naziru Ahmad Sarkin waka a gaban kotun Majistrate mai lamba 58 dake zaman ta a unguwar Noman's Land a jihar Kano karkashin mai Shari'ah Aminu Muhammad Gabari bisa tuhumar sa da fitar da wa su wakoki biyu da ya yi ba tare da izinin hukumar ba.
A watan Satumbar shekarar da ta gabata ne hukumar ta fara gabatar da Naziru Sarkin Waka da tuhumar a gaban kotun Majistrate dake zaman ta a yankin Rijiyar Zaki daga bisani kuma ta maiyar da shari'ar zuwa kotu mai lamba 16. Sai dai kuma sakamakon sauye-sauyen da Kotu nan su ka samu a a ka mayar da shari'ar Kotun Noman’s Land.
Sai dai Naziru Sarkin wakar ya musan ta tuhumar da a ke yi masa a ranar Larabar nan bayan da a ka karanta masa tuhumar sa, sai dai a nan Lauyan da ya ke kare shi ya roki Kotun da ta sanya shi a hannun beli ta kuma amince ta sanya shi bisa sharadin cewa sai mahaifin sa ya tsaya masa ko wakilin mahaifin ko kuma mai unguwar su ko ma wani jami'in hukumar Hisba.
Kotun ta kuma tsayar da ranar daya ga watan Disamba mai kamawa na wannan shekarar, domin ci gaba da shari’ar

Labarai masu kamanceceniya