“Duk Wanda Hukuma Ba Ta Tantance Shi Ba Ya Daina Yin Fim A Kano”

[email protected] 2019-09-11 10:25:15 Tattaunawa

A kokarin da sashen yada labarai na Northflix ke yi, ya tattauna da Shugaban Kungiyar masu shirya finafinan ta Arewa Filmmakers reshen jihar Kano Alh. Jamilu Ahmad Yakasai, inda ya yi tsokaci kan batun tantance ‘yan fim.

Kwanaki kun kai ziyara ga Sarkin Bichi, Alhaji Aminu Ado Bayero, menene makasudinta?

Da farko dai ziyarar ba ni na shiryata ba, Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano ita ta shirya, sai ta ga ya kamata ta gayyaci wani cikin masu ruwa da tsaki musamman kungiyarmu ta Arewa. Shugaban Hukumar, Ismail Na’Abba Afakallah ne ya gayyace mu, inda muka ziyarci Sarki, kuma muka tattauna da shi.

Tun kafin mu tafi ya sanar damu cewar makasudin ziyarar da za a kai don ana so a samar tare da kara inganta gidajen kallo a wadannan kananan hukumomin dake karkashin masarautarsa. Akwai kananan hukumomi guda goma da suke karkashin masarautar Bichi, za a bibbisu duka domin karfafa cewar dukkan me gidan kallo na a wadannan kananan hukumomi dake haska finafinanmu, za a bullo da tsari wanda furodusa zai rika amfana.

Alhamdulillah an je tare da mu kuma an gabatar da mu a gaban mai martaba Sarki cewar ana tafe tare da wadannan shugabanni, kuma Sarki ya yi maganganu masu dadi, don ba mu taso ba sai da ya baiwa hakimansa izinin cewar dukkan abinda muka zo da shi na assasa gidajen kallo a kananan hukumominsu da su bamu hadin kai, su tsaya tsayin daka su shiga cikin lamarin su taimaka mana don ganin abubuwa sun tafi yadda ya kamata.

Mai Martaba Sarki Ya yi mana alkawarin cewa idan akwai fim din da muke sha’awar nuna domin al’umma su fadakartu, mu zo kofar gidansa, mu yi amfani da magiji don nuna wa jama’a tare da wayar musu da kai.

Akwai tsari da aka bullo da shi na tantance ‘yan fim, ya ya kake kallon lamarin?

Hakika an dade ba a zowa masana’antar nan da tsari mai kyau kamar wannan ba, domin duk inda aka ce tantancewa ana so a fitar da wani abu daga cikin wani abu ne, don haka muma muke so mu fitar da baragurbi daga cikin masana'antar fim. Me ye baragubi? Mutanen da ba su cancanta ba ko suke da wani mugun hali, ko kuma suke jawo mana ka-ce-na-ce da zagi da hada husuma.

Wannan ya sa gwamnati ta ga dacewar bin tsarin tantancewa, mu ga wai su waye ma ya kamata su zama masu sana'ar fim, su waye suka cancanta, sannan su waye ba su cancanta ba a cire su. Gwamnati ta kara da cewar za ta bamu goyon bayan cewar duk mutumin da bai cancanta ba, ko kuma mutumin da ba shida ingancin ya zama me sana'ar fim, ko ba shida tarbiyyar da ya kamata ya zama ne sana'ar fim, indai aka cire shi za a bada goyon baya a tabbatar da cewar ya ciru ba kuma zai kara sana'ar film ba a jihar Kano.

Bayan harkar tantacewa akwai wasu matakai da kuke bi don tsaftace harkar film?

Ai ita kanta tantancewar mataki ce ta tsaftace harkar fim, saboda ta wannan tantancewar ake so a fitar da duk wasu abubuwa da suke kawo nakasu ko kuma su jawo kyamata daga al'umma, so muke duk a karkade a tsince duk mutanen da suke da kima sannan suka dace suke da inganci su zama su ne a cikin sana'ar fim, don haka wannan ai yana cikin tsaftace sana'ar film. Tantacewar ita zata tabbatar da tsaftacewar insha Allah.

Kuna samun cikakken hadin kai daga wajen wadanda ake son tantacewa?

Mutane da yawa suna ta tururuwar zuwa ana tantace su domin gwamnati ta yi rantsuwar cewar daga karshen watan Satumba, duk wanda ba a tantance shi ba ba zai kara yin fim a jihar Kano ba, domin tana kokari ne akan dukkan matsalolin da ake samu acikin wannan sana'a su daidaita, wannan ya saka mutane suka amsa kira ake ta zuwa ba dare ba rana don tantancewa, don haka sai dai mu godewa Allah, mutane suna bada gudunmawa sosai, suna zuwa kuma suna kan zuwa, wasu da ba su fahimta ba da yanzu su ma a hankali sun fara fahimta kuma suna bamu goyon baya don haka maganar hadin kai ana samu mun gode Allah.

Me yasa siyasa ta yi tasiri a cikin masana'antar kannywood?

Siyasa yau ta zama ba cikin kannywood kadai ba, a cikin gida ma ta ratsa ta shiga, yau siyasa ta zama dakin mahaifiyarka da kuke zaune da kai da dan uwanka, sai ka ga wani yana can wani yana can, don haka siyasa ta zama ko ina babu inda ba ta kutsawa ta shiga tunda har na bada misali da gidaje.

Ala kulli halin, nan bangaren mu na masu shirya finafinai, musamman ni da nake shugaba na Arewa Filmmakers, muna ta kokarin mu gudanr da abubuwa ba tare da nuna banbanci ko siyasa ko wani abu ba, mu abinda muka sani mu masu jagoranci ne kuma muna da 'ya'ya daga ko wane bangare na siyasa, ya zama dolen mu basu kulawa daidai wa daida, don kana wancan bangare ko kana wancan tsagi wannan ra'ayinka ne, mu a nan bangaren sana'armu babu bambancin siyasa, maganace ta duk dan kungiya ka bashi hakkinsa yadda ya kamata, kuma muna iya kokarinmu wajen wancakalar da siyasa, ba muna nufin in kana kungiya ba kada ra'ayin yin siyasa, siyasar ka daban kungiya daban, kuma ba za ka shigo da al'amuran siyasarka kungiya ba, domin ita kungiya ta kowa ce.

Labarai masu kamanceceniya