Masu Garkuwa Da Mutane Ba Su Yi Min Fyade Ba – Maryam KK

[email protected] 2019-11-27 01:54:33 Tattaunawa

A kwanakin baya ne masu garkuwa da mutane su ka sace sabuwar jarumar Kannywood Maryam K.K. Mun samu tattauna da ita don samun cikakken bayani kan bun da ya faru.

Kwanki kin gamu da iftila’in da ya faru da ke, ko za ki yi mana Karin haske?

Wata rana na je aiki Kaduna, Sunusi oscer ya kira ni da daddare a waya kan cewar akwai aiki a Abuja yana so na zo. Na fada masa cewar a lokacin ina Kaduna amma insha Allah da safe zan taho tunda lokacin dare ya yi.

Washe gari da safe na tafi Abuja kamar yadda na yi wa Sunusi Oscar alkawari. Bayan mun gama aikin na shirya na tafi gida duk da shawartata da abokan aikina suka yi kan na kwana domin lokacin dare ya fara yi amma na ki domin ina da uzuri.

Na fito bakin titi ina jiran me mota taxi, motar da ta fara zuwa bamu daidaita ba sai a mota ta biyu wacce ita ce silar faruwar al'amarin.

Lokacin da me motar ya tsaya na fada masa inda zani ya amince, ya fito ya dauki jakata tare da samun a but, sannan ya bude mun motar na shiga.

Lokacin da na shiga da mutum biyu a cikin motar daya a gaba daya a baya daga gefena.

Bayan da muka fara tafiya ne muka shiga duhu, sai na gaban ya danne ni da kujerar mota na gefen kuma ya shaqe min wuya sannan suka fara duka na.

Daga nan sai me ya faru?

Sun kwace wayoyina tare da umarta ta da in cire musu password din. Bayan da na bude ne suka fara duba min hotuna sannan suka duba sakonnin ciki, suka ga sakon da banki suka turo min, da nawa da kuma na me wayar (asalin wanda ya bani wayar) suka tambayeni ATM dina nace musu yana cikin jakata (wacce dama tana hannunsu) suka dauko ATM din nawa guda biyu suka tambayeni lambarsa, shi ma na fada musu. Sannan suka tambayeni da waye da waye nake ganin za a samu kudi a hannunsu. Suka ciro wuka da bindiga sannan suka zuba guba a jikin hankici suka ce za su kashe ni idan ban fada musu ba.

Na ce musu ba ni da kowa da za a samu kudi a hannunsa, jin hakan ya sa suka cigaba da dukana, sai shi wanda ya amshi wayar tawa ya fara duba kiran da aka yi min.

Lambar Darakta Sunusi Oscar ita ce ta farko, hakan ya sa suka neme shi sannan suka cigaba da neman mutane, suna fada musu cewar ina wajensu kuma suna so a tura musu kudi, idan an tura za su sake ni, idan kuma ba a tura ba zasu kashe ni ko su sayar da ni.

A cikin haka suka samu lambar yayana suka yi magana da shi sannan suka nemi na ba su lambar asusuna na banki, na ba su sai suka ce a turo musu dubu dari a lokacin.

Duk wayoyin da suke ba a gabana suke ba don ban ma san dawa dawa suke waya ba. Sai dai lokacin da suka cewa yayana ya turo musu dubu 100 ta account dina sun yanke ni a wuya.

Bayan daya turo kudin ne kuma suka dauke ni suka tafi da ni inda za su kai ni. Anan na tadda mutane da yawa wanda gabadayansu 'yan mata ne. Kuma bayan ni suka cigaba da kawo wasu 'yan matan. Gaba daya wadanda suke kawowa 'yan mata ne babu manya.

Miliyan hamsin shi ne abinda suka fadama yayanmu suke da bukata, saidai sun cigaba da ciniki har suka qarqare a miliyan biyu.

Yaya kika tsinci kanki a wannan lokacin?

Fargaba da tsoro sannan babu kwanciyar hankali babu ruwa babu abinci. Na tsora ta sosai saboda an zo an sissiyi 'yan mata da yawa a gabana. Kuma masu siyan 'yan yankan kai ne, matsafa, da mashaya jini.

Na tsorata sosai domin duk yarinyar da suka kama suka nemi kudi ba a kai ba suna siyar da ita. Haka muka cigaba da zama cikin dar-dar kowa yana tunanin makomarsa ga duka ga wahala ga kuma azaba.

Ta ya ya aka yi kika kubuta?

Sun gama ciniki da yayanmu kan miliyan biyu suke so a basu. Suka fada masa inda zai ajje kudin sannan suka ce sai sun tabbatar da yakai kudin za su taimake ni. Kwana na biyu yayana ya kawo musu kudin kamar yadda ya yi alkawari.

Suka ce na fito sannan suka saka ni a cikin mota, muka je inda babu mutane, ba tare da mun tsaya ba suka bude motar suka tunkudani suka wuce. Ban tsira da komai ba sai jakata wadda suka zazzage komai dake cikinta.

Bayan 'yan uwana sun zo sun dauke ni ne muka wuce ofishin ‘yan sanda, daga nan muka tafi banki sannan muka kuma komawa ofishin ‘yan sanda kafin mu tafi asibiti, sannan ‘yan jarida suka zo suka yi hira da ni.

Me za ki ce game da yadda mutane suka rika kallon lamarin?

Bayan na ji sauki kuma na fara fuskantar kalubale daga mutane inda aka dinga yada jita-jita, wasu su ce karya nake, wasu su ce hada baki na yi da mutanen, wasu kuma su ce neman kudi kawai nake, kadan ne daga cikin mutane suka yarda da ni.

Tunda abin ya faru bana cikin kwanciyar hankali, ga tsoro da fargabar abinda na fuskanta ga kuma surutun mutane. Gabadaya tunda na fito rayuwata ta canja ko yaushe cikin firgici nake da tashin hankali. Kuma ana yawan tura min text ana tsoratar da ni wanda ban san ko su waye ba.

Ni yanzu ina rayuwa ne, amma kamar a mace nake, domin na daya ina cikin baqin ciki, na biyu hankalina bai kwanta ba, sannan na uku ina cikin fargaba da tsoro.

Labarai masu kamanceceniya